Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

NAFDAC: An rufe gidajen ruwan leda a Sokoto

Published

on

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ta rufe wasu gidajen da suke samar da ruwan leda 38 sakamakon karya dokokin yin kasuwanci a jihar Sokoto.

Shugaban hukumar a jihar Malam Garba Adamu ne ya bayyana hakan, yayin zantawar sa da manema labarai.

Ya ce, sama da ledar ruwa dari uku ne aka kama, a ƙananan hukumomi 23 waɗanda kuma sun yi rijsta sai dai sun saɓa doka.

Malam Garba Adamu ya ce, matakin ya biyo bayan ayyukan da hukumar ta fara a ranar 19 ga watan da muke ciki, don kiyaye lafiyar al’umma ta hanyar abubuwan da suke saya don amfanin su, da kuma tabbatar da sun bi dokokin da NAFDAC ke sanyawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!