Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun cafke gawurtaccen mai garkuwa da mutane a kano – Bijilanti

Published

on

Rundunar tsaron Sintiri na Bijilante reshen jihar Kano ta ce, ta cafke wani mutum da ya jima yana yin garkuwa da mutane.

Babban Kwamandan rundunar na jiha Muhammad Kabir Alhaji ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

A cewar sa, sun kama mutumin mai suna Sada Lawal ne a garin Gomo da ke ƙaramar hukumar Sumaila a lokacin da ya yi ɓadda-bami a cikin almajiran wata makaranta.

Muhammad Alhaji ya ce, binciken su ya gano cewa, Sada Lawan ya jima yana addabar mutane ta hanyar garkuwa da su a yankin Sumaila da kewaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!