Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Corona: mutum 131 ne suka kamu da corona – NCDC

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce a jiya Litinin an samu karin masu dauke da cutar corona anan Najeriya da yawansu ya kai dari da talatin da daya.

Wannan adadi na cikin rahoton da hukumar ke wallafawa a shafinta na Twitter a kowacce rana sai dai a yau babu rahoton asarar rai.

A cewar NCDC jihohi goma sha hudu ne suka samu karin masu dauke da cutar ciki har da birnin tarayya Abuja.

Anan Kano ma, ma’aikatar lafiya ta jihar tace an samu kari mutane bakwai masu dauke da cutar corona a litinin din nan, cikin gwaji da aka yiwa mutane 26.

Wannan dai ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kai dubu dari da sittin da daya, da dari takwas da ashirin da biyar, ciki kuwa mutane dubu dari da arba’in da takwas, da dari daya da ashirin da biyar sun warke sarai.

Sai kuma wadanda suka rasu sanadiyyar cutar da yawansu ya kai dubu biyu da talatin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!