Labarai
Mun cafke motoci maƙare da Giya- KAROTA
Hukumar Kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta jiha Kano KAROTA, ta samu nasarar kama motoci guda hudu kirar J5 maƙare da Barasa.
Shugaban Hukumar KAROTA Faisal Mahmud Kabir, ne ya bayyana haka a daren jiha
Lokacin da yake duba motocin bayan da jami’an Hukumar suka sami nasarar cafke motocin
Ya ce, hukumar KAROTA ta samu nasarar kama motocin ne bayan rahoton sirri da ta samu a wajen wasu masu kishin jihar Kano
Ya ƙara da cewa dokar jihar Kano ta haramta shan giya a ko wanne lokaci, musamman yanzu da ake cikin wata mai alfarma
Ya kara da cewa Ya zama wajibi Hukumar ta rubanya kokarinta wajen sa ido a daukacin titinan jihar Kano.
A karshe ya yaba wa jami’an da suka cafke motocin.
Ya kuma ce, da zarar an kammala binciki za a mika Giyar Hukumar Hizba domin ta kara fadada bincike tare da daukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login