Ƙetare
Mun daƙile juyin mulki- Sojojin Kongo
Dakarun sojin Jamhuriyar dimokraɗiyyar Kongo, sun bayyana cewa, sun daƙile juyin mulkin da wasu ‘yan ƙasar da na ƙetare suka kitsa wa shugaban ƙasar Felix Tshikedi a Kinshasa babban birnin ƙasar.
BBC ta ruwaito cewa, ta cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin ɗin ƙasar, mai magana da yawun sojojin ƙasar Burgediya Janar Sylavin Ekenge, ya ce a yanzu ƙura ta lafa, kuma sojojin ƙasar na tsare da wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Haka kuma ta bayyana cewa, Jawabin nasa na zuwa ne sa’o’i bayan da wasu mutane ɗauke da makamai suka afka gidan tsohon shugaban ma’aikata kuma babban aminin shugaban ƙasar, da safiyar ranar Lahadi.
Shaidu sun ce ga wasu mutane kimanin 20 sanye da kayan sojoji sun afka wa gidan sannan suka ji ƙarar harbe-harben bindiga.
Sai dai kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce maharan mambobin wata ƙungiya ce da ake kira ‘New Zaire Movement’ mai alaƙa da ɗan siyasar ƙasar da ke zaman gudun hijira a ƙetare, Christian Malanga.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar masu gadin gidan biyu da mahari guda.
You must be logged in to post a comment Login