Barka Da Hantsi
Mun datse ruwan kogin Haɗeja da jama’are ne domin inganta noman rani – Ma’amun Da’u
Hukumar raya kogunan Haɗeja da Jama’are ta ce an datse ruwan kogunan ne domin inganta noman rani da kuma gyaran madatsun ruwa da fadama.
Hukumar ta kuma ce ambaliyar ruwan da ake samu a gonaki bashi da alaƙa da kogunan, sai dai ana alaƙanta ambaliyar da hukumar ne saboda su ke kula da ɓangaren ruwa.
Shugaban hukumar Ma’amun Da’u Aliyu ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
“Bazai yiwu mu yi aiki ruwa na gudana a magudanan ruwan mu ba hakan ya tilasta mana ɗaukar matakin datse ruwan.”
“Bamu datse ruwan kogin Hadeja da jama’are ba sai da muka zauna da shugabannin ƙungiyoyin manoma suka amince da a datse ruwan domin inganta harkar noma, sannan mun bada sanarwa a kafafan yaɗa labarai kafin a rufe ruwan tare da tura wakilanmu lungu da sako don sanar dasu datse ruwan.”
Ma’amun Da’u ya kuma ce nan da watan mayun shekarar 2022 za’a buɗe madatsun ruwan domin ci gaba da amfani da su.
You must be logged in to post a comment Login