Labarai
Mun fasa tafiya yajin aiki – NUPENG
Kungiyar direbobin dakon man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG ta janye yajin aikin da kuduri aniyar farawa a ranar litinin, bayan da gwamnatin tarayya ta sanya baki a ciki.
Shugaban kungiyar mai kula da shiyyar Kudu maso yammacin kasar nan Tayo Aboyeji ne ya tabbatar da hakan jiya a Lagos, inda ya ce sun fasa tafiya yajin aikin don samun damar tattauna da gwamnatin tarayya kan bukatunsu.
NUPENG ta ce ta yi asarar mambobinta da dama da kuma dukiyoyi masu tarin yawa sakamakon rashin kyawun manyan titunan kasar nan, wannan shi ne dlailin da ya sa za su shiga yajin aikin.
A jiya ne dai kamfanin mai na kasa NNPC, ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Garba Deen ya yi kira ga kungiyar ta NUPENG, da ta dakatar da wannan kuduri na shiga yajin aikin a ranar Litini.
Sanarwar ta ce kamfanin ya bijiro da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen magance matsalar lalacewar manyan titunan kasar nan cikin hanzari.
You must be logged in to post a comment Login