Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun gano inda jirgin yakin mu ya yi hatsari – Rundunar sojin saman Najeriya

Published

on

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce akwai fargabar cewa jirgin soji na yaki mallakinta da ya yi batan dabo a ranar laraba, akwai bayanan da ke tabbatar da cewa, ya yi hatsari ne.

A cewar mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward gabkwek, ba a san dalilin da ya yi sanadiyar hatsarin ba, kuma ba a san inda matuka jirgin biyu suke ba.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa, ta ce, matuka jirgin sune: Flight Lieutenant John Abolarinwa da kuma Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele.

Sanarwar ta kuma ce, rundunar sojin sama ta Najeriya tuni ta bazama don gano inda matuka jirgin suke.

Jirgin yakin sojin mai dauke da mutane biyu a cikinsa, an daina jin duriyar sa ne tun da misalin karfe biyar na maraicin ranar Laraba.

A cewar rundunar tun farko an tura jirgin ne don taimakawa dakarun kasar nan da ke fafatawa da ‘yan boko haram a jihar Borno.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!