Connect with us

Labarai

Mun haramta sanya bakar leda a gilashin gaban mota – Sufeton ‘Yan sanda

Published

on

Sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba ya sanar da dakatar da amfani da bakar leda a gilashin gaban mota wato Tinted a fadin kasar nan.

Usman Alkali Baba ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin ganawa da manyan jami’an ‘yan sanda ciki har da manyan mataimakan sufeto janar da kwamishinoni a sassan kasar nan.

Ya ce, umarnin ya fara aiki nan take, har ma ya ce rundunar ta haramta rufe hanyoyi ba bisa ka’ida ba.

Alkali Baba ya gargadi shugabannin kwamandojin kasar nan da cewa dole ne su sanya idanu don hana rufe hanya ba bisa ka’ida ba da kuma samar da dabarun da za a rika amfani da su a madadin rufe hanyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!