Connect with us

Labarai

Hukumar kwallon kafa ta Brazil ta dakatar da shugaba Rogerio Caboclo

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil CBF, Mr. Rogerio Caboclo ya fuskanci hukuncin dakatarwa na wucin gadi bisa zargin cin zarafin mata.

Hukumar da’a ta CBF ta dai dakatar da Mr. Caboclo tsawon kwanaki 30.

Ana zargin Mr. Caboclo da laifin yunkurin yin lalata da wata ma’aikaciyar hukumar, inda ya kuma musanta zargin da ake yi masa.

A bisa ka’idar kundin tsarin mulkin hukumar wanda ya baiwa mataimaki damar maye gurbin shugaba koda wani abu ka’iya faruwa, yanzu haka Antonio Carlos zai maye gurbin Mr. Caboclo a matsayin shugaban hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!