Labarai
Mun janye zanga-zangar da za’a bayan mun cimma matsaya -NLC
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta janye zanga-zangar lumana da ta yi niyyar gudanarwa a Jihar Rivers sakamakon cimma yarjejeniyar da kungiyar ta yi da gwamnatin tarraya.
Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ayuba Wabba.
A cewar sanarwar, kungiyar ta janye zanga-zangan lumanan ne bayan ta yi nassara akan gwamnatin tarraya kan mafia karaci albashi ga ma’aikatar gwamnatin jihar Rivers.
Ta cikin sanarwar, kungiyar za ta tabbatar da ci gaba da kare hakkin ma’aikata a fadin kasdar.
You must be logged in to post a comment Login