Labarai
Mun kafa kwamitin duba iftila’i a Najeriya – Sadiya Farouq
Gwamnatin tarayya ta ce ta kafa kwamitin da zai rika duba yawan afukar iftila’i da samar da hanyoyin rage afukawarsa a fadin kasar nan.
Ministar kula da al’amuran jin kai da kare afukar iftila’I, Hajiya Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan lokacin da take jawabi ga mambobin kwamitin jiya a birin tarayya Abuja.
Sadiya Umar Farouq ta ce samar da kwamitin zai taimaka wajen kula da abubuwan da ke haifar da Ifti’lan dake afkuwa a kasar nan musamman matsalar ambaliyar ruwa.
An daura auren Sadiya Farouq da Air Marshal Sadiq Abubakar
Wadanda suka nemi N-Power sun kai miliyan 4
Hadakar kwamitin da Ministan ta kafa, sun hadar da ma’aikata a hukumar kula da al’amuran jin kai da kare afkuwar iftila’I da ma’aikata a ma’akatar samar da ruwan sha da ma’aikatar Gona sai ma’aikatar Muhali da ma’aikatar yada labarai. Da dai sauransu.
You must be logged in to post a comment Login