Ƙetare
Mun kai wa wani jirgin dakon mai hari a mashigar Hormuz – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan wani jirgin dakon mai na wata ƙasar yankin Gulf da ya ratsa ta mashigar Hormuz.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Telegram, ta ce jirginta maras matuƙi ne ya kai wa jirgin dakon man hari, saboda ”watsi da gargaɗin bi ta mashigar da runudunar IRGC ta sha yi”.
Rundunar IRGC ta ƙara da cewa ba za ta bari jiragen dakon mai da na kasuwanci ”masu ƙawance da ”ƙasashen da muke faɗa da su” su bi ta mashigar ba.
Zirin Hormuz na ɗaya daga cikin hanyoyin jigilar makamashi mafiya muhimmanci a duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wurin zuwa kasuwanni.
Yaƙin da ake yi a Iran ya haifar da nakasu ga harkar safarar mai a yankin Gulf, bayan da gwamnatin Iran ta yi baranazar ƙona duk wani jirgin dakon mai da ya yi yunƙurin wucewa ta wurin.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ”idan ta kama” sojojin ruwan Amurka za su riƙa yi wa jiragen rakiya don su wuce ta wurin.
You must be logged in to post a comment Login