Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun fara biyan mutanen ƴan sabo diyyar su – Dr. Kabiru Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan kuɗaɗen diyya ga al’ummar yankin ‘yan Sabo a karamar hukumar Tofa.

Diyyar dai ta biyo bayan karɓar gonakin da kuma gidajen su da aka yi, sakamakon aikin samar da madatsar ruwa da ya biyo ta kan su.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ta tabbatar da biyan na su, a zantawar sa da Freedom radio ta cikin shirin “Barka da Hantsi”.

Ya ce, “ biyan diyyar yana da tsari, saboda mutanen su kusan ɗari biyu da biyar ne, kuma mun biya mutum dari da saba’in diyya, saura talatin da biyar kuma a cikin su za mu biya su kuɗin a satin nan” inji Getso.

Dakta Getso ya kuma ce, dukkanin waɗanda lamarin ya shafa da su yi hakuri bisa jinkirin rashin biyan su a kan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!