Labarai
Mun kammala shirin gudanar da zaben cike gurbi na Kano- INEC

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC na Kano Abdu Zango, ya tabbatar da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar, wanda za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Zaben zai gudana ne a kananan hukumomin Bagwai, Shanono, tsanyawa da kuma karamar hukumar Ghari.
Zango Abdu ya bayyana cewa an tanadi isassun kayan aikin zabe, ma’aikata, gami da samar da tsaro, domin tabbatar da gudanar da zabe cikin gaskiya, adalci, da lumana, ba tare da tashin hankali ko tafka magudi ba.
Ya kuma yi kira ga ‘yan takara, jam’iyyun siyasa, da masu kada kuri’a, su gudanar da harkokinsu cikin natsuwa da mutunta dokokin zabe, tare da gujewa duk wata dabi’a da za ta iya kawo cikas ga zaman lafiya a lokacin zabe.
You must be logged in to post a comment Login