Labarai
Mun kammala shirye-shiryen zaɓen cike gurbi na kansiloli- KANSIEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta ce, ta kammala dukkan shirye-shiryen ta domin gudanar da zaɓen cike gurbi na kansiloli a mazabun Kofar Mazugal da Matan Fada da ke cikin kananan hukumomin Dala da Ghari.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kan ta, ta kano Farfesa Sani Lawan Mulumfashi ne ya bayyana hakan a yau biyo bayan rasuwar kansilolin da ke wakiltar waɗannan mazabun biyu, inda hukumar ta bayyana cewa zaɓen zai gudana ne bisa tanadin sashi na 30 na dokar zaɓe ta shekara ta 2022.
Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya kara da cewa zaɓen cike gurbin zai gudana a ranar 13 ga watan Disamba, shekara ta 2025, kuma sun tabbatar da shirin su na gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Hukumar ta kuma mika sakon ta’aziyya ga Gwamnatin jihar Kano da kuma al’ummmar kananan hukumomin Dala da Ghari bisa wannan rashi na jagororinsu.
You must be logged in to post a comment Login