Labarai
Mun karbo sama da Naira biliyan 566 cikin shekaru biyu da suka gabata- EFCC

Shugaban hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa, EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta karbo sama da Naira biliyan 566 cikin shekaru biyu da suka gabata.
Mista Olukoyede ya ce, wannan nasarar ta kasance ne sakamakon matakan da hukumar ta dauka wajen aiwatar da dokokin yaki da rashawa, karbo kadarori, da kuma inganta tsarin aiki a cikin gwamnati.
Shugaban hukumar ya kuma yi alkawarin cewa EFCC za ta ci gaba da aiki tukuru wajen dakile ayyukan rashawa da satar dukiyar jama’a a kowane mataki na gwamnati
You must be logged in to post a comment Login