ilimi
Mun kashe fiye da Miliyan 484 wajen gyara makarantu 1,200- Kwamishinan Ilimi

Gwamnatin Kano ta ce ta kashe fiye da Naira Miliyan dari hudu da tamanin da hudu wajen gyara makarantu fiye da guda dubu daya da dari biyu a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashin yada labarai na ma’aikatar Ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar kan taron tattauna karawa juna sani ga ma’aikatan dake fannin Ilimi da ma’aikatar Ilimi ta shirya musu na kwana daya.
Sanarwar ta ce, a jawabin kwamishinan Ilimi na Kano Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce, gwamnati ta hada kai da Kansilolin mazabu 484 da aka gudanar da aikin a mazabunsu, wanda ya kasance irinsa na farko a tarihi da aikin ya lashe fiye da naira miliyan dari hudu da Tamanin.
Kwamishinan ilimin ya bayyana hakan ne yayin bikin bued bada horon kara sanin makamar aiki da aka shirya wa jami’an ma’aikatan ilimi da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tabbatar da inganci da kuma nagartar aiki.
Dakta Ali Haruna Makoda, ya kuma ce, “Duk da cewa Kano na da kimanin makarantu 30,000, lamarin da ke nuna cewa ita ce ta fi yawan makarantu, amma gwamnati na yin iyakar kokarinta wajen tabbatar da cewa, ta na bayar da ingantacce ilimi.”
You must be logged in to post a comment Login