Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kashe ‘yan ta’adda a jihar Katsina – Rundunar ‘yan sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe ƴan ta’adda 15 tare da ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Sanusi Buba ne ya bayyana hakan jiya Alhamis yayin wani taron manema labarai a shalkwatar ƴan sanda ta jihar.

Sanusi Buba ya ce, rundunar ƴan sandan ta yi nasarar kama waɗanda ake zargin ƴan ta’adda ne sama da 50.

Ya ƙara da cewa, ƴan sandan sun kuma yi nasarar ƙwato bindigu guda 9 samfurin AK 47, da na gargajiya guda 20, da kuma motoci guda 2 da babura 20.

Haka kuma sun samu ƙwato shanun da aka sata 220, haɗe da kuɗi tsaba har naira dubu 685,000 daga ƴan ta’addar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!