Labarai
Mun kwato kudade sama da Naira miliyan 500 a Kano – Muhuyi
Hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano, ta sanar da kwato kudade sama da Naira Miliyan 500 a fadin jihar.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema Labarai da aka gudanar a ofishin hukumar.
Muhuyi Magaji ya ce an shirya taron ne domin bayyana ayyukan hukumar dangane da nasarorin data samu da kalubale, a shekarar 2020, da Kuma farkon watanni Uku na shekarar 2021.
“Mun Karbi korafe-korafe sama da 2,000 wadanda kaso 70 cikin Dari an samu nasarar ayyukan su, mun kwato Filaye sama da 400, tare da samun nasarar hana boye Man Fetur da Kayayyakin Abinci don kara musu farashi da kuma kwato kayan abincin Tallafin Corona da aka boye a wasu guraren,” inji Muhuyi.
Muhuyi ya kuma ce, “Duk da nasarorin da muke samu, hukumar na fama da kalubalen katsalandan daga wasu masu rike da madafun Iko da kuma manyan mutane dake neman hana Ruwa gudu a ayyukan mu, a gefe Daya akwai matsalolin kudaden gudanar da wasu ayyuka a fadin kananan hukumomin jihar 44.”
Haka zalika, hukumar tasha alwashin fadada ayyukan ta tare da aiki kafada-da-kafada da hukumomin ICPC da EFCC da sauran kungiyoyin ayyukan cigaba don yin aiki ga al’ummar jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login