Connect with us

Labarai

Wani jirgin yaki yayi batan dabo a jihar Borno

Published

on

Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya ya bace sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi jihar Borno kamar yadda hukumomi suka bayyana a safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar Sojin Saman Najeriya, air Commodore Edward Gabkwet, ya ce jirgin Alpha din ya kauce hanyar sa ne tun a ranar Laraba da misalin karfe 5 na yamma.

Har kawo ranar Alhamis ba a kai ga gano shi ba, sakamakon na’urar da ke hango zirga-zirgar jirage ta gaza gano inda ya shiga, sai dai Commodore Edward yace ana ci gaba da bincike.

Jirgin da ya bace ya na tsaka da aikin samar da tsaro ga sojojin kasa, don dakile ayyukan masu tayar da kayar baya.

Wannan dai na zuwa ne makonni kadan bayan da wani jirgin Sojan Saman kasar nan, ya yi hadari sakamakon gazawar injin sa a kan hanyarsa zuwa Minna ta Jihar Neja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives