Labarai
Mun shirya tsaf don kare abkuwar ambaliyar ruwa a Kano – Dr Getso
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta shirya tsaf don daukar matakan da suka dace na dakile faruwar ambaliyar ruwa a daminar bana.
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Duniyar mu Ayau na nan tashar Freedom.
Shirin Duniyar mu a yau na wannan rana ya mayar da hankali ne kan batun masu harkar ma’adanan a jihar Kanon ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ke haifar da matsalolin muhalli ciki har da ambaliyar ruwa.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce akwai dalilai da dama da suke haifar da ambaliyar ruwa ciki kuwa har da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
“Akwai illa mai tarin yawa ga wadanda suke dibar ma’adanan kasa ba bisa ka’idaba,bwanda kuma hakan kan iya jefa al’ummar da ke rayuwa a yankin cikin halin damuwa, musamman zaftarewar kasa, ambaliyar ruwa da sauran matsalolin muhalli,” inji Getso.
Getso ya kuma ce kowanne albarkatun kasa na da guba mai illa musamman ga kananan yara ta fannin shafar kwakwalwar su da sauran sassan jiki.
“Rashin ilimi hakar ma’adanai shi yake janyo duk wata barazana ga muhalli wanda kuma nan ba da dadewa ba za mu kawo karshen matsalar” kamar yadda kwamishinan muhalli ya bayyana.
You must be logged in to post a comment Login