Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kananan asibitoci 239 ne zasu fara karbar tallafin kudi a Jigawa – Badaru

Published

on

Kimanin kananan asibitoci 239 ne zasu fara karbar tallafin kudi ta cikin sabon shirin bayar da maguguna kyauta ga rukunin mata masu juna biyu da kananan yara da kuma tsofaffin wanda Gwamnatin tarayya ta billo da shi.

Babban sakataren lafiya na jihar Jigawa Dr. Salisu Mu’azu ne ya bayyana haka ya yin taron kaddamar da fara mika kudin ga hukumomin asibitocin, har ma ya hore su wajen aiwatar da abin ta hanyar da ta kamata.

Wakilinmu daga Dutsen jihar Jigawa Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, Dr, Salisu Mu’azu  na cewa wannan na daya daga cikin alkawuran da gwamnatin jihar ta dauka don saukakawa marasa galihu wajen siyan  maguguna ya yin da basu da lafiya bayan da wasu daga cikin asibitocin jihar suka cika ka’idojin shiga shirin.

Yana me yin kiran ga alu’mma da su yi amfani da kudin ta hanyar da dace, ba tare da sun karkatar da shi ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!