Manyan Labarai
Mun warware korafe-korafe masu dinbim yawa- Muhyi Magaji
Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa hukumar ta karbi dinbim korafe-korafen al’ummar jihar Kano, da ta samar musu mafita a shekarar da ta gabata.
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai, a sakatariyyar ‘yan jaridu dake nan Kano.
Ya ce shakka babu hukumar tayi amfani da tanade-tanaden doka wajen gurfanar da wadanda ake zargi da laifukan cin hanci da rashawa a sassan jihar Kano daban-dabam.
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya kuma bukaci al’ummar garin Kano da su rungumi dabi’ar amfani da guraben da gwamnatin Kano ta ware don saka koken su kan abubuwan da suke faruwa ba dai-dai ba a jihar don daukar matakin gyara.
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano na kira wajen neman goyon bayan al’ummar jihar Kano, tare da basu cikakkun bayanai don gudanar da ayyukan su.