Labarai
Mun yi haɗin gwiwa da shugabannin kasuwannin waya don gano masu yin kwace – DSP Kiyawa
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta yi haɗin gwiwa da kasuwannin sayar da wayoyin hannu domin su riƙa samun bayanan masu ƙwacen waya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi”na nan Freedom Radio.
“Mun lura cewa kaso 70 ciki 100 na masu ƙwacen waya a jihar Kano suna ta’ammali da miyagun ƙwayoyi”.
“Wannan ne ya sanya muka ga dacewar yin haɗin gwiwa da shugabannin kasuwannin waya, domin su rikƙa ba mu rahoton wayoyin da ake kasuwancin su, kasancewar masu ƙwacen suna kai wa kasuwa domin su sayar” a cewar Kiyawa.
Kiyawa ya kuma ce, a kwanakin nan rundunar ta na samun nasarar kama masu ƙwacen waya musammana a ƙwaryar birnin Kano.
You must be logged in to post a comment Login