Connect with us

Labarai

Mun yi wa ma’aikatan bogi tayin afuwa -Tambuwal

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi wa ma’aikatan bogi fiye da dubu  takwas afuwa da masu karbar albashi da ya wuce guda daya afuwa.

Hakan na kunshe cikin sanararwar da Kwamishinan kudi na jihar Alhaji Abdussamad Dasuki ya bayyana a ya yin wani taro da manema a birnin Sokoto.

Alhaji Abdulssamad Dasuki ya kara da cewar gwamnatin jihar ta dauki matakin ne don karfafawa ma’aitan da ke wannan mumunan halin da su tunawa kan su asiri, ba tare da gwamanti da kwarmata su ba ko kuma ta tuzarata su ba.

APC zata daukaka kara kan shari’ar zaben gwamnan Sokoto

SOKOTO:Asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo sun fara tiyatar zuciya

Gamayyar Jam’iyyun ashirin sun ki amincewa da nasarar gwamnan jihar Sokoto

Kazalika ya ce, ma’aikatan gwamnatin da suke karbar albashin da da suka bayyana wannan mumunan halin a asirice to babu shakka gwamnati zata yi musu afuwa.

A cewar Kwamishinan kudin Alhaji Abdulssamad Dasuki za a rufe karbar afuwar ne a ranar tara ga watan Disambar mai kamawa

 

Coronavirus

Covid-19: Babu hawan sallah a Kano

Published

on

Maimartaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’ummar Kano da su kiyaye dangane da yanayin da ake ciki na annobar Covid-19 da ta janyo sauyawar al’adun fada.

Sarkin ya bayyana hakanne a daren Asabar a Kofar Kwaru yayin da yake jawabi a gaban manyan hakiman sa kan yadda za a gudanar da sallar bana.

Maimartaba Aminu Ado ya ce babu hawan sallah na al’ada da masarautar Kano ta sabayi duk shekara saboda yanayin Corona.

Sarkin ya kara da cewa maimakon hakan Sarki zai tafi idi a kafa, inda zai fito ta kofar Fatalwa har zuwa filin idi na Kofar Mata da safe.

Bayan an idar da sallar idi kuma Sarkin zai biyo ta unguwar Kofar Wambai da Zage, sannan ya biyo ta Dorayi da Shahuci daga nan ya zarto zuwa Kofar Kwaru a Mota.

Ana sa ran Sarkin zai yi jawabi ga al’ummar Kano bayan sakkowa daga sallar idin a Kofar Kwarun kamar yadda al’adar masarautar Kano take.

Wakilinmu na fadar sarkin Kano Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito mana cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa al’ummar Kano sakamakon rashe-rashen da aka samu sannan yayi fatan marasa lafiya Allah ya basu lafiya.

A karshe Sarkin yayi kira ga al’ummar Kano da su cigaba da kiyayewa tare da yin biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya wajen dakile yaduwar cutar Corona.

A shekarun baya dai, kafin annobar Covid-19 ta bullo akan shafe kwanaki biyar ana gudanar da hidimomin al’ada na masarautar Kano a yayin bikin karamar sallah.

Hoton Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.

Continue Reading

Labarai

Ana shagulgulan karamar sallah yau a Nijar

Published

on

Al’ummar jamhuriyar Nijar sun bi sahun takwarorin su daga kasashen musulman duniya wajen shagulgulan salla karama.

A jiya ne dai majalisar musulunci ta kasar ta fitar da sanarwar ganin jinjirin watan a wasu sassan kasar wanda hakan ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadan.

Tun da sanyin safiya ne dai al’ummar musulmin kasar suka yi fitar dango dan halartar masallatan idi.

Da misalin karfe 9 na safe ne, Limamin babban masalacin Idi ya jagoranci sallah raka’a biyu kamar yadda addinin musulunci ya tanada kafin daga bisani ya gabatar da huduba da harshen larabci.

Bayan haka suma daya bayan daya gwamnonin jihohi da mai martaba sultan na Damagaram sun gudanar da wani takaitaccen jawabin barka da salla ga al’ummar jihar.

Wannan sallah dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da cutar Covid-19 lamarin kuma da ya rage armashin sallar masamman ga magidanta da ke kukan rashin kudi.

Wakilinmu Yakuba Umaru Maigizawa ya rawaito mana cewa za’a ci gaba da bukukuwan karamar sallar har nan da kwanaki uku masu zuwa kamar yadda aka saba a al’adance.

Ku kalli hotunan yadda sallar idi ta kasance:

Continue Reading

Coronavirus

Ranar Lahadi za ayi Sallah a Zaria – Sarkin Zazzau

Published

on

Maimartaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya ce ranar Lahadi itace ranar Sallah a garin Zaria.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Freedom Radio ta samu a daren Juma’a tace masarautar bata umarci al’umma su ajiye azuminsu a ranar Asabar ba.

Sanarwar ta kara da cewa Sarkin Zazza na umartar al’umma da suyi biyayya ga umarnin mai alfarma Sarkin musulmi wanda shine Allah ya dorawa hakkin bada sanarwar ganin wata, kuma tuni ya sanar za ayi sallah ranar lahadi.

A daren Juma’a ne aka rika yamadidi da wasu rahoronni a kafafan sada zumunta kan cewa Sarkin Zazzau ya bada sanarwar a ajjye azumi ranar Asabar.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,276 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!