Connect with us

Labarai

Mun zargi ‘yan siyasa da yin wadaka a shirin daukar aiki na matasa – Kungiya

Published

on

Kungiyar Matasan Kano ta zargi ‘yan siyasa da yin watandar raba wadanda za’a dauka aiki a nan Kano kar kashin shirin daukar aiki na gwamnatin tarayya dubu dubu dari 774 a nan Kano.

Akan haka ne kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ministan kwadago da su kawo dauki kan wannan batun, wajen dakatar da shirin a nan Kano.

Hakan na kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da shugaban kumgiyar Kwamarred Ibrahim Waziri da sakatariya Aisha Haruna Kabuga suka sanya wa hannu cewa, sun rubuta wasikar koke ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don kawo dauki kan wannan wadaka da ake zargin ‘yan siyasar sun yi wa shirin daukar aikin a nan Kano.

 

Sai dai da dai sakataren kwamitin anan Kano Abubakar Muhammad Janaral da muka tuntube shi kan batun ya ce shi a halin yanzu ba ya cikin kwamitin

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!