Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Yawan wadanda suka kamu da cutar Korona ya kai dubu 49895

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce a jiya Talata an samu karin wadanda suke dauke da cutar corona a kasar nan su dari hudu da da goma.

Hakan na cikin sanarwar da NCDC ta wallafa a shafin ta na Twitter a daren jiya inda ta ce mutane hudu sun rasu a sanadiyyar cutar.

Yanzu haka dai kasar nan a da adadin wadanda suka kamu da cutar da yawan su ya kai dubu arba’in da tara da dari takwas da casa’in da biyar cikin gwaji da aka yiwa mutane dubu dari uku da hamsin da biyar da dari daya da casa’in da shida.

A cewar sanarwar da NCDC ta wallafa a shafin ta na Twinteer wadanda suka kamu da cutar  dari 410 sun fito ne daga jihohi 16 har da babban birnin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!