Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an tsaro sun gayyaci masu shirya zanga-zanga a Kano

Published

on

Jami’an tsaro sun gayyaci matasan huɗu cikin jagororin da suka shirya zanga-zanga a Kano.

Jagoran masu zanga-zangar a Kano Sharu Ashir Nastura ya shaida wa Freedom Radio cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro sun gayyace su tun ƙarfe goma na dare kuma ba a sallame su ba har sai bayan ƙarfe uku na dare.

Nastura ya ce, sun shirya zanga-zangar ne domin neman lallai gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin arewacin ƙasar nan.

“Muna buƙatar wannan sabon sashen na ƴan sanda (SWAT) a kawo su yankunanmu da ake fama da matsalolin tsaro domin su yaƙi ƴan ta’adda a cewar Nastura.

Wata majiya rundunar tsaron farin kaya ta DSS reshen Kano ta ce sun gayyaci masu shirya zanga-zangar ne domin tsara musu yadda zasu gudanar da zanga-zangar bisa tsarin doka.

Koda muka tuntuɓi rundunar ƴan sandan Kano, mai magana da yawunta DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bai samu labarin ba, amma zai bincika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!