Labarai
Muna aiwatar da sabbin tsare-tsare a fannin kiwo- Gwamna Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya bayyana cewa, gwamnatinsa na aiwatar da tsare-tsare na musamman domin inganta harkar kiwon dabbobi da samar da madara, tare da kawar da gibin ababen more rayuwa da kuma jawo hankalin masu zuba jari a fannin domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya ce su zuba jarin Euro miliyan goma domin kafa sabuwar gonar samar da madara a Damau, da ke ƙaramar hukumar Kubau, wadda za ta fara aiki a mataki farko nan ba da jimawa ba.
A cewar sa, wannan shiri zai taimaka wajen bunkasa samar da madara cikin gida, tare da ƙarfafa manoman dabbobi da masu kiwo, da nufin rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje.
You must be logged in to post a comment Login