Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna Allah wadai ga Alƙalan da suke bayar da umarnin a saki kwayoyin da aka kama

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata tabbatar ta kai alƙalan da suke bayar da Court order ga hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa Karota, kan kama kwayoyi da hukumar ta kama domin wannan rashin kishin al’umma ne.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yau Asabar yayin ziyarar bazata da gwamnan yakai hukumar karota domin ganin yadda aikin hukumar ke gudana da kuma yadda za’a ƙara inganta musu kayan aikin su.

Gwamna Yusuf ya kuma kara da cewa yanzu haka zasu tabbatar sun bayyana sunayen duk wasu alƙalan da suka bayar da wannan umarnin na sakin kayan da aka kama.

Haka kuma gwamnan ya ƙara da zarar an tabbatar da alkalan da suke bayar da order gwamnati zata tabbatar ta ayyana sunan su da kuma sanya sunan su da kwayoyin da aka kama a gidajen jaridu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa hukumar Karota bisa yadda suke gudanar da aikin su yadda ya kamata kuma gwamnan yasha alwashin ƙara inganta musu kayan aiki musamman motocin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!