Connect with us

Kasuwanci

Muna asarar tumatir a wannan lokaci – Ƴan kasuwar ƴan Kaba  

Published

on

Wani ɗan kasuwar kayan miya da ke ƴan Kaba ya kokawa kan yadda suke asarar tumatir a wannan lokaci.

Lawan Abdullahi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

Ya ce, “Mu ƴan kasuwar kayan miya muna tafka asara a kowacce rana musamman ta tumatir, samakamon yadda yake saurin lalacewa”.

“A kowacce rana muna tafka asara ta maƙudan kuɗaɗe da mu kan mu ba mu san adadin sa ba, wannan ne ma yake mayar da kasuwancin mu baya” in ji Lawal.

Lawan Abdullahi ya kuma ce, a baya kamfanin Dangote na sayen tumatir ɗin su don sarrafawa tare da rage musu asara, sai dai a yanzu ba sa samun wannan damar.

Sai dai ya buƙaci gwamnati da ta samar musu da hanyar da za su riƙa kai tumatir ɗin nasu ana sarrafawa.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!