Labarai
Muna bincike bisa kisan Ango- Yan Sandan Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce tana bincike kan kisan wani ango da aka tsinci gawarsa cikin jini a gidansa da ke unguwar Tashar Buja a Karamar Hukumar Jibia.
wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa an samu rahoton cewa an sami wani ango kwance cikin jini da ciwo a wuya, kuma aka garzaya da shi asibiti inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Sanarwar ta ce an kama mutum guda da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin kisan.
You must be logged in to post a comment Login