Connect with us

Manyan Labarai

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kwato Shanu sittin

Published

on

Rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina, ta sanar da kashe dan garkuwa da mutane, gudan daya tare da kwato shanu sittin.

Rundunar  ta sanar da kubutar da Shanu sittin da Tumaki tamanin a wani kwantan bauna da tayi wa ‘yan garkuwa da mutane da suka farwa Kauyen Karo da Garangamawa a karamar hukumar Dutsin ma ,ta jihar.

A wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar Sufeto Gambo Isah, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, ta tabbatar dacewa rundunar ta samu rahoton cewar ‘yan garkuwa da mutane dauke da bindigogi kirar AK 47, sun shiga kauyukan da karfe biyun daren jiya Laraba, tare da kai hari kan garuruwan.

Labarai masu alaka.

An kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Katsina

Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina

Sanarwar ta kara dacewa Jim kadan bayan samun labarin Babban jami’in ‘yan sanda na Dutsinma , ya umarci tawagar musamman ta Operation Puff Adder, tare da ‘yan sintiri na Unguwar Bara, wajen kai samame ga yan ta’addar.

A harin kwantan baunan, jami’an sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan wanda a ciki suka samu nasarar kashe daya daga cikin ‘yan garkuwa da mutane tare da kwato  shanu sittin da tumakai tamanin.Haka kuma tawagar ta cigaba da sintiri da duba mabuya  daban -daban a cikin dajin, don neman wanda suka tsere da harbi a jikin su ,tare da kwato makaman su ,tare da fadada bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!