Labarai
Muna buƙatar tsari na samar da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam a Kano – UDHR
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Universal Declaration of Human Right da ke Kano ta ce, samar da yawan ƙungiyoyin kishin al’umma a Kano shi ke haifar da ƙaruwar ɓatagari a cikin ƙungiyoyin.
Shugaban ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin taron da kungiyar ta gabatar kan tattauna hanyoyin da za a bi na tantance ƙungiyoyin kishin al’umma a Kano.
Yama ce da yawa daga cikin ƙungiyoyin a yanzu sun mayar da aikin su neman kuɗi ba tare da taimakon al’umma ba, kamar yadda manufar su take a baya.
Ya ce “yanzu haka ƙungiyoyin kishin al’umma a Kano sun fi guda Hamsin wanda kuma ƙalilan ne daga cikin su suke gudanar da aikin su yadda ya kamata”.
“Dole ne a fito a samar da matsaya kan yawan buɗe ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam don inganta ayyukan taimakon jama’a musamman marasa ƙarfi”.
Tuni dai ƙungiyoyin suka fara karawa ƙudirin baya domin kuwa shugaban kungiyar Global Community of Human Right, Karibu Yahaya Lawal Kabara, ya nuna goyon bayansa kan matakin.
Har ma ya ce “tsarin zai samar da daidaito, kuma abin maraba ne ga ci gaban ƙungiyoyin”.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na yin ruwa da tsaki wajen ƙwayowa al’umma haƙƙin a inda aka take musu hakkin su ko aka fi ƙarfin su.
You must be logged in to post a comment Login