Labarai
Muna da ƙarancin ma’aikatan shara a Kwalejin Fasaha – Dakta Isyaku
Kwalejin fasaha ta jihar Kano wato School of Technology ta koka kan rashin isassun ma’aikatan kula da tsaftar muhalli.
Daraktan kwalejin Dakta Isyaku Ibrahim ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar duban tsaftar muhalli.
Dakta Isyaku wanda Malam Yusuf Maitama ya wakilci shi ya ce, “Muna da ƙarancin ma’aikatan shara a kwalejin dalilin kenan da ya sa aka ga kwalejin babu tsafta a yau”.
“Muna da ƙarancin masu shara kuma ba za su wadata wajen share dukka kwalejin gaba ɗaya ba, amma suna iya ƙoƙarin su na ganin sun yi shara”. a cewar Dakta Isyaku.
Wannan dai na zuwa ne yayin da Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kai ziyarar duban tsaftar muhalli na ƙarshen wata a Lahadin nan.
Getso ya ƙalubalanci mkwalejin bisa rashin tsaftar muhalli da ya tarar, har ma ya gargaɗe ta da ta ɗauki matakin gyara kafin ya sake waiwayar ta.
You must be logged in to post a comment Login