Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A koyi matakan yaki da corona daga kwalejin tsaftar muhalli – Dakta Getso

Published

on

Kwamshinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bukaci sauran makarantun jihar Kano da su yi koyi da kwalejin koyar da harkokin tsaftar muhalli don yaki da cutar corona.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce matakin da kwalejin ta dauka abin alfahari ne don kuwa cikin dokokin yaki da cutar corona babu wanda suka bari a baya.

A cewar sa “matukar al’umma musamman makarantu za su dauki irin wadannan matakan babu shakka za a yaki cutar corona cikin sauki”.

A don haka ya bayyana farin cikin sa ga shugaban kwalejin Dakta Bashir Bala Getso kan irin jajircewarsa kan harkokin tsaftar muhalli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!