Labarai
Muna da cikakkiyar amincewa da rundunar sojin- Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce tana da cikakkiyar amincewa da rundunar sojin kasa, ta na mai cewa babu wani yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamar yadda wasu kafafen labarai suka wallafa.
Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai inda ya kara da cewa gwamnati ba ta da wani dalili da zai sa ta yi shakku da bayanin da shalkwatar tsaro ta fitar, wadda ta bayyana rahoton da aka wallafa na yunkurin juyin mulkin a matsayin ƙarya.
Tun a ranar Asabar din da ta gabata ne dai, mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce, kama jami’an soji 16 da ake zargi, ba na juyin mulki ba ne, illa binciken ladabi na cikin gida domin tabbatar da da’a da bin doka a rundunar.
Sai dai wasu jam’iyyun adawa, sun bukaci gwamnati da rundunar sojin su bayyana gaskiya kan ainahin abin da ya faru.
You must be logged in to post a comment Login