Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Muna kan-bakar-mu na fara yajin aiki a gobe – NLC

Published

on

Gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar nan na NLC da TUC sun sha alwashin fara yajin aikin da ta kuduri aniya a gobe litinin sakamakon karin farashin man fetur da wutar lantarki a kasar nan, duk da sanya bakin da majalisar wakilai ta yi a yau domin dakatar da shi.

Da safiyar yau ne dai shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya yi wata ganawar sirri ta kusan sa’a guda da shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Kwamared Ayuba Wabba da takwaransa na TUC Quadri Olaleye.

Sauran mahalarta taron sun hadar da mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar Peter Akpatason da shugaban kwamitin Kwadago na majalisar Ali Muhammad.

Bayan kammala taron ne Ayuba Wabba ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatin tarayya da kanta ta sabawa umarnin kotu wajen yin karin farashin wutar lantarkin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!