Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba mu taba kama Abdurrashid Bawa da laifin cin hanci da rashawa ba- EFCC

Published

on

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce sabon shugaban hukumar da aka nada bashi da wani rahoto da ya nuna an taba kama shi da laifin cin hanci da rashawa.

 

A cewar hukumar ba ta taba samun Bawa da wani laifi da ke da alaka da cin hanci da rashawa ba, ko kuma cefanar da kadarorin gwamnatin.

 

Wannan dai na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Mr. Wilson Uwajaren.

 

Sanarwar ta ce, hakan ya biyo bayan wani rahoto da wasu jaridun Internet ke yadawa cewar Abdurrashid Bawa na daya daga cikin masu hannu cikin laifukan da aka kama tsohon shugaban hukumar Ibrahim Magu da su na cefanar da wasu kadarorin gwamnatin da yawan su kai dari biyu da arb’in da hudu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!