Labarai
Muna kira ga gwamnati da a samar mana da ruwan sha – kantoman Tudun wada
Shugabancin riƙo na ƙaramar hukumar Tudun Wada ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da tayi duba da irin halin da al’ummar yankin suke ciki na rashi ruwa da huta domin kawo musu ɗauki.
Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Alhaji Umar Isah Ahmad ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai kan irin halin da ƙaramar hukumar da yake jagoranta take ciki.
Shugaban ya kuma ce wannan matsalar da ƙaramar hukumar take ciki ta dauki shekaru tana fuskantar hakan in har kawo wannan lokaci an kasa shawo kan matsalar, adan haka suke kira ga gwamnatin jihar Kano data kawo musu sauyi a wannan lokaci.
Alhaji Umar ya kuma ce lokacin da ya karɓi jagoranci ƙaramar hukumar ya same ta ne cikin mawuyacin hali la’akari da rashin hanyoyin zirga-zirga taɓarɓarewar harka noma a yanki da dai sauran su.
Haka yayin da muka fara shiga ofishi mun fara gudanar da wasu ayyukan da zasu farfaɗo da martabar ƙaramar hukumar, wajen neman tallafi ga ɗai ɗai kun jama’a masu kishin yankin da gwamnati, domin itama ƙaramar hukumar ta sami sauyi a wannan lokacin, A cewar Shugaban.
Akwai abitoci a faɗin ƙaramar hukumar da aka gina su tsahon shekaru amma har kawo wannan lokacin basa gudanar da aiki, shiyasa a wannan lokaci muyi yunƙurin samar da magunguna da dukkannin abubuwan da ake bukata a cikin asibiti domin wa’innan Asibitoci su fara aiki, domin kulawa da lafiyar al’ummar yankin.
Matsalar ruwa sha da take a yankin a yanzu haka mun yi rubutu mun turawa gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin bamu da matsalar da tafi wannan a yankin mu domin rashin ruwa ba ƙara matsala bace a cikin al’ummah.
Kuma yanzu haka muna fatan gwamna zaiyi duba da irin wannan koke da al’ummar yanki suke yi domin kawo musu daukin gaggawa.
Akwai kanfanoni da ma’aikatu da suke son su samar da su a cikin ƙaramar hukumar amma rashin huta ya hana, wanda da ace akwai huta a da hanyoyi a yankin da tuni ƙaramar hukumar Tudun Wada takai ga ci inda zata zama abar kwatance a jihar kano harma da ƙasa baki ɗaya, Duk a Cewar shugaban riko na ƙaramar hukumar.
Haka kuma zamu tabbatar mun shigewa al’ummar yankin Tudun Wada musamman matasa wajen samar musu da aikin yi musamman yadda gwamnatin jihar kano take tallafawa mata da matasa a faɗin jihar.
Haka kuma shugaban yayi anfani da wannan damar wajen taya Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara ɗaya akan karagar mulki, inda yake fatan gwamnatin Abba zata ci gaba da ɗorawa kan manyan ayyukan da zasu ingata rayuwar al’umma da ciyar da jihar Kano gaba.
You must be logged in to post a comment Login