Labarai
Muna samun gagarumar nasara wajen dakile shaye-shaye a Kano- NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA, shiyyar Kano, ta ce tana samun gagarumin nasara a yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Mai magana da yawun hukumar a Kano, Sadik Muhammad Mai Gatari, ne ya bayyana haka a wata tattaunawarsa da Freedom Radio.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da hada kai da kungiyoyin masu zaman kansu wajen fadakar da al’umma kan illolin shan miyagun kwayoyi, domin samar da al’umma nagari.
You must be logged in to post a comment Login