Labarai
Muna tattaunawa da hukumomi domin a dawo da Walida – Gwamna Namadi

Gwamnanatin jihar Jigawa a ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta don ganin an saki yarinyar nan Walida Abdulhadi ƴar asalin jihar da ake zargin wani jami’in DSS da sace ta tare da sauya mata addini.
Cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar ya ce gwamnatin jihar na ɗaukar lamarin da matuƙar muhimmanci, sakamakon irin tausayin da labarin ke ɗauke da shi.
Batun Walida na ci gaba da ɗaukar hankalin ƴan Najeriya, inda ƙungiyoyin fararen hula ke ci gaba da kiraye-kirayen yi wa yarinyar adalci.
Tun da farko dai an zargi wani jami’in DSS ta sace yarinyar daga jihar Jigawa tare da tilasta mata aurensa har ta haihu da kuma sauya mata addini.
A watan da ya gabata ne dai wata kotu a ƙasar ta bayar da umarnin sakin Walida tare da sada ta da iyayenta, to sai dai har yanzu tana ci gaba da tsare a hannun hukumar DSS.
Gwamnatin jihar ta ce ma’aikatar shari’ar jihar na biye da batun yarinyar domin tabbatar da an bi duka matakan shari’ar da suka dace cikin doka.
”Ma’aikatar na aiki da hukumomin da lamarin ya shafa domin kare ƴancin yarinyar”, a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnan jihar da kansa tare da wasu manyan gwamnatin jihar sun tuntubi hukumomin da lamarin ya shafa domin tabbatar da adalci cikin lamarin.
You must be logged in to post a comment Login