Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Muna taya Al’ummar Kano murnar zagayowar watan Maulidi- Com. Aminu Abdussalam

Published

on

Mataimakin gwamnan jihar Kano Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar haihuwar ma’aiki SAW

Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci al’ummar musulmai da suyi koyi da irin ɗabi’un Manzon Allah domin samin dacewa nan duniya da kuma gobe ƙiyama.

Kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana hakan ne ta cikin wata takarda da mai magana da yahun sa Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar ya kuma rabawa manema labarai

Gwarzo ya kuma ce zai yi amfani da wannan damar domin wajen yin kira ga al’ummar jihar kano wajen yin anfani da wannan lokacin domin neman zaman lafiya kyautawa juna haɗin kai domin samar da ci gaba ga al’ummar jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!