Labarai
Sanatoci sun fitar da sunan sabon shugaban babban bankin CBN

Majalisar dattawa ta tabbatar da Olayemi Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya CBN.
Shugaban Majalisar ne ya bayyana hakan yayin zaman da majalisar tayi don tantance wadanda suka cancanta a matsayin shugaban babban bankin, da mataimakansa a yau.
Haka zalika majalisar ta tabbatar da mutane hudu a matsayin mataimakan gwamnan da suka hadar da Emem Nnana Usoro da Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Philip Ikeazor da Kuma Bala Bello.
You must be logged in to post a comment Login