Coronavirus
Munaneman a kara mana cibiyoyin gwajin Corona a Kano-P4CS
Kungiyar hadin kai da kuma kare al’umma wato Partners for Community Safety, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da karin ci boyiyin gwajin cutar Corona a jihar Kano, la’akari da yadda jihar Kano ke da dumbin mutane.
Shugaban kungiyar, Kwamared Ali Wali ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai game da yadda gwajin cutar ta Corona ke gudana a Kano.
Kwamared Ali Wali ya kuma bukaci cibiyar dakile cutuka ta kasa NCDC da ta samar da kayan aikin da suka kamata na gwajin cutar ta Corona a nan Kano, domin ganin an magance yaduwar ta.
Tsagaita dokar Zirga-Zirga: Bankuna sun cika makil a Kano
NNPC ta tallafawa Kano da kayan yakar Coronavirus
Kwamared Ali Wali ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro dasu kara zage dantse wajen gudanar da ayyukan su na hana shige da fice a jihar Kano, a cewar sa har yanzu akwai rahotannin da ake samu cewa a na samun wadan da ke shigowa jihar Kano ta barauniyar hanya.
Shugaban kungiyar ya kuma yi kira ga al’umma da malamai da shugabanni da su baiwa gwamnati hadin kan da ya kamata domin ganin an magance cutar ta Corona a Kano.
You must be logged in to post a comment Login