Labarai
Musulmai na zanga-zangar ƙyamar Faransa a Kano
Al’ummar musulmi na gudanar da zanga-zangar nuna ƙyamar Faransa a birnin Kano.
Masu zanga-zangar sun fara tattaki da misalin ƙarfe 12 na ranar Lahadi daga Unguwar Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala.
Jagoran masu zanga-zangar Kwamared Mukhtar Nalele ya ce, ya zama tilas su nuna fushi kan kalaman ɓatanci da shugaban Faransa ke yiwa musulunci.
Nalele ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su ƙaurace wa sayen kayan ƙasar Faransa domin yin tir da abin da ke faruwa.
Masu zanga-zangar a Kano na ɗauke da kwalaye waɗanda aka rubuta saƙonnin nuna ƙyama ga Faransa da shugabanta.
Me shugaban Faransa ya yi?
Jawabin shugaba Macron na cewa zai yaƙi addinin musulunci, shi ne ya fusata al’ummar musulmin duniya.
Jawabin ya biyo bayan kisan wani malamin makaranta mai suna Samuel Paty wanda ya nuna wa ɗalibansa zanen da aka yi na ɓatanci ga Annabi Muhammad (s.a.w).
Ƙasashen musulmi da dama ne suka shiga yin Alla-wadai tare da suka kan kalaman na Faransa.
Ƙaurace wa kayan Faransa ya fara tasiri
Faransa ta buƙaci kasashen Gabas ta tsakiya da ka da su amince da kiraye-kirayen ƙaurace wa sayen kayayyakinta.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ce ta bayyana hakan, wanda ke nuna fargaba kan fara ƙaurace wa kayayyakin nata.
You must be logged in to post a comment Login