Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Mutane 12 sun rasa ransu sakamakon hadarin mota a Kaduna

Published

on

Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane 12 sakamakon haɗarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Shugaban hukumar shiyyar Kaduna Hafiz Muhammad ne ya bayyana hakan, yayin zantawar sa da manema labarai.

Ya ce, hatsarin ya faru da misalin karfe 12 na ranar Litinin, kuma mutane 12 sun rasa ran su, sai kuma 6 da suka jikkata sakamakon fashewar tayar motar.

Hafiz Muhammad ya kuma ce, motar da hatsarin ya faru ta yi lodin fasinjoji fiye da ƙima, abinda ya haifar da hatsarin a hanyar Nasarawa Doka zuwa Kacia.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!