Labarai
Mutane 146 sun mutu sakamakon zazzabin Lassa daga Janairu zuwa Maris- NCDC

Gwamnatin Tarayya ta ce akalla mutum 146 ne suka mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa daga watan Janairu zuwa tsakiyar Maris na shekarar nan da muke ciki ta 2026.
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ce ta bayyana hakan ne a cikin rahoton mako na 11 na yaduwar cutar da ta wallafa a shafinta na Internet wanda ya kunshi bayanai daga ranar 9 zuwa 15 ga watan Maris.
A cewar hukumar, adadin mace-macen ya kai kaso sama da 25, cikin dari a bana, wanda ya fi na shekarar 2025 da ya tsaya a kaso sama da 18, cikin dari.
NCDC ta ce yawan masu kamuwa da cutar ya karu daga mutum 40 a mako na 10 zuwa mutum 66 a mako na 11, lamarin da ke nuna yadda cutar ke kara yaduwa a wasu sassan kasar.
Rahoton ya nuna cewa an samu karin yaduwar cutar ne a jihohin Taraba, Filato, Edo, Benuwe, Kogi, Gombe da Neja.
Hukumar ta kara da cewa zuwa yanzu an samu bullar cutar a kananan hukumomi 82 da ke cikin jihohi 21 a fadin kasar.
Sai dai jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benuwe da Edo ne ke dauke da kaso mafi yawa na masu dauke da cutar, inda suka kai kashi 85 cikin dari na jimillar wadanda suka kamu a shekarar 2026.
You must be logged in to post a comment Login