Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Mutane 30 sun mutu cikin mako guda sanadiyyar cutar Corona a Lagos – Sanwo-Olu

Published

on

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ce cutar Corona da ta sake dawowa karo na uku ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a cikin mako guda a jihar.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin da yake bada bayanai kan bullar cutar karo na uku samfurin Delta ga manema labarai a Lagos.

Ya ce, ana samun akalla mutuwar mutane shida a kowace rana cikin makon da ya gabata.

“Duk da haka bai kamata a mayar da hankali kan fargaba da firgici ba, amma ya kamata mu mayar da hankali tare da tsayayyiyar azama da jajircewa don sauya yanayin”, in ji shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!